Rahotanni daga Ƙaramar Hukumar Mariga ta Jihar Neja sun nuna cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hare-hare a garuruwan Kumbashi, Kakihum da Maburya.
Shafin Comrd Yarima Bk ne ya wallafa rahoton da safiyar Laraba, yana mai cewa maharan sun kwashe wayoyi, kuɗi da wasu kayayyakin jama’a, tare da yin garkuwa da wasu mutane.
Rahoton ya kuma yi zargin cewa ɗaya daga cikin maharan ya yi amfani da wata wayar da aka sace wajen wallafa hotonsa da aika saƙon murya a ƙungiyar WhatsApp ta Mariga Development Forum.
Lamarin ya zo ne duk da rahotannin da ake samu game da ƙoƙarin samar da sulhu a wasu yankunan da ke fama da hare-haren ’yan bindiga.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Labarinmu bai samu sanarwar hukuma daga rundunar ’yan sandan Jihar Neja da za ta tabbatar da adadin mutanen da aka sace ko cikakken barnar da harin ya haifar ba.
Za mu sabunta wannan labari da zarar hukumomi ko shugabannin yankin sun bayar da ƙarin bayani.
An sha samun hare-hare da sace-sacen mutane a Mariga; a watan Fabrairun 2026, ’yan sanda sun tabbatar da ceto mutane goma da aka yi garkuwa da su bayan artabu tsakanin jami’an tsaro da masu garkuwa.



