Majalisun jihohi 30 sun amince da gyaran kundin tsarin mulki kan ‘yan sandan jihohi — Akpabio

Akpabio ya ce kusan majalisun jihohi 30 sun amince da gyaran kundin tsarin mulkin kafa ‘yan sandan jihohi, amma tsarin bai fara aiki ba tukuna.

Akpabio ya ce kusan majalisun jihohi 30 sun amince da gyaran kundin tsarin mulkin kafa ‘yan sandan jihohi, amma tsarin bai fara aiki ba tukuna.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, bayan hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI, ta jinjinawa Najeriya kan hadin gwiwar yaki da wata kungiyar masu aikata laifukan cin zarafin yara…

Rahotanni sun ce gamayyar jami’an tsaro da ƙungiyoyin sa-kai sun dakile harin ’yan bindiga a yankin Karfi da ke Ƙaramar Hukumar Malumfashi, Jihar Katsina.

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike tare da kamo waɗanda suka kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, da abokinsa Adamu Abubakar a Dutsin-Ma, Jihar Katsina.

Rahotanni daga Ƙaramar Hukumar Mariga ta Jihar Neja sun ce ’yan bindiga sun kai hare-hare a Kumbashi, Kakihum da Maburya, inda aka ce sun sace mutane tare da kwashe kuɗi, wayoyi da wasu kayayyaki.

Hukumar NEMA ta ce aƙalla mutum 62 ne suka mutu, wasu 52 suka jikkata, yayin da dubban mazauna suka rasa matsugunansu bayan harin Binnari a Jihar Taraba.