An tabbatar mutanen da ake zargin sun kamu da Ebola a Adamawa ba su da cutar — NCDC

NCDC ta tabbatar cewa gwaje-gwaje biyu da aka yi wa mutanen da ake zargin sun kamu da Ebola a Adamawa sun nuna ba su da cutar.

Hukumar Dakile Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa mutane biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a Jihar Adamawa ba su da cutar.

Babban Daraktan NCDC, Dakta Jide Idris, ya ce an gudanar da gwajin dakin bincike har sau biyu, kuma dukkan sakamakon ya nuna cewa mutanen ba su kamu da Ebola ba.

Rahoton zargin ya fito ne daga birnin Yola bayan mutanen biyu sun nuna wasu alamomin rashin lafiya masu kama da na Ebola. Hukumomin lafiya suka killace su tare da daukar samfuransu domin gudanar da bincike.

NCDC ta ce tana aiki tare da gwamnatin Jihar Adamawa domin gano hakikanin abin da ya jawo rashin lafiyar. Hukumar ta bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, su kuma guji yada bayanan da ba a tabbatar da su ba.

Ta shawarci duk wanda yake fama da zazzabi, matsananciyar kasala, ciwon kai, amai, gudawa ko zubar jini ba tare da dalili ba—musamman bayan mu’amala da wanda ake zargin yana dauke da cutar—ya garzaya asibiti.

NCDC ta ce za ta ci gaba da sanya ido tare da fitar da sabbin bayanai idan bukatar hakan ta taso.

Aika wannan labarin