Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tabbatar cewa ba za ta sauya ranakun babban zaben Najeriya na 2027 ba, tana mai cewa shirye-shiryenta suna tafiya bisa jadawalin da aka fitar.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan a taron da ya gudanar da jami’an hukumar da kwamishinonin zabe na jihohin Kudu maso Kudu a Fatakwal, Jihar Ribas.
Amupitan ya ce wa’adin da doka ta tanada tabbatacce ne, kuma za a gudanar da zabukan kamar yadda aka tsara. Ya yi wannan bayani ne bayan rade-radin cewa ana iya dage babban zaben.
Bisa jadawalin INEC, za a gudanar da zaben shugaban kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa a ranar 16 ga Janairu, 2027. Za a gudanar da zabukan gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.
Shugaban hukumar ya ce INEC tana aiki da hukumomin tsaro domin kare masu kada kuri’a, ma’aikatan zabe da kayayyakin aikin zabe.
Ya kuma gargadi jami’an INEC da ma’aikatan wucin gadi cewa duk wanda aka samu yana kokarin gurbata tsarin zabe zai fuskanci matakin doka.
Amupitan ya ce ‘yan Najeriya ne za su zabi shugabanninsu, ba fasahar kirkirarriyar basira ko wasu manhajojin kwamfuta ba. Sai dai ya amince cewa akwai barazanar hare-haren yanar gizo, yana mai cewa hukumar za ta karfafa tsaron na’urori da bayananta.




