Adadin waɗanda suka mutu a harin Binnari na Taraba ya kai 62 — NEMA

Hukumar NEMA ta ce aƙalla mutum 62 ne suka mutu, wasu 52 suka jikkata, yayin da dubban mazauna suka rasa matsugunansu bayan harin Binnari a Jihar Taraba.

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa, NEMA, ta bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kai wa al’ummar Binnari a Ƙaramar Hukumar Karim-Lamido ta Jihar Taraba ya kai aƙalla 62.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, lokacin da maharan suka afka wa garin tare da buɗe wuta kan mazauna. Wasu rahotanni sun ce harin ya zo ne a ranar kasuwar mako, inda ’yan kasuwa da jama’a daga garuruwan da ke kewaye suka taru.

Shugaban NEMA na Jihar Taraba, Ladan Ayuba, ya ce harin ya kuma jikkata mutum 52 tare da tilasta wa dubban mutane barin gidajensu. Hukumar ta ce an ci gaba da gano gawarwaki a wurare daban-daban, ciki har da waɗanda aka ciro daga Kogin Benuwai.

Tun farko, rundunar ’yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutum 10. Sai dai adadin ya ƙaru zuwa 40, daga bisani 58, yayin da jami’an tsaro da mazauna yankin suka ci gaba da gano ƙarin gawarwaki a dazuzzuka da cikin ruwa. Rahoton PREMIUM TIMES ya ce cikin waɗanda aka tabbatar sun mutu akwai mutum 15 da suka nutse yayin ƙoƙarin tserewa a cikin kwale-kwale.

Kakakin rundunar ’yan sandan Taraba, Victor Mshelizah, ya bayyana cewa adadin bai kai matsayinsa na ƙarshe ba, domin har yanzu ana ci gaba da aikin nema da tattara bayanai.

Rahotanni daga garin sun kuma nuna cewa an ƙona wasu gidaje da shaguna, tare da kwashe abinci, kuɗi da babura. Har yanzu babu wata ƙungiya da ta fito fili ta ɗauki alhakin harin.

Gwamnatin Taraba ta miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, tare da bayyana aniyarta ta ƙara matakan tsaro domin hana sake afkuwar irin wannan hari.

Aika wannan labarin