Adadin man fetur, dizal da man jiragen sama da Matatar Dangote ta fitar zuwa kasashen waje ya zarce wanda aka karba a kasuwar Najeriya a watan Satumban 2026.
Bayanai daga rahoton Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Tsakiya da Kasa (NMDPRA) sun nuna cewa matatar ta fitar da lita miliyan 54.63 na wadannan nau’o’in mai a kowace rana.
A daya bangaren, adadin da aka karba domin kasuwar cikin gida ya kai lita miliyan 39.98 a rana. Hakan na nufin fitar da man kasashen waje ta zarce na cikin gida da lita miliyan 14.65 a kowace rana.
Adadin man da aka fitar ya karu da kashi 37.33 cikin dari idan aka kwatanta da watan Agusta. Na kasuwar cikin gida kuma ya ragu da kashi 22.08, daga lita miliyan 51.31 zuwa miliyan 39.98 a rana.
Sai dai man jiragen sama ne ya fi haifar da wannan banbanci. Idan aka hada fetur da dizal kawai, adadin da aka kai kasuwar Najeriya—lita miliyan 36.64 a rana—ya fi lita miliyan 31.38 da aka fitar kasashen waje.
Rahoton ya nuna cewa Matatar Dangote ta samar da lita miliyan 47.22 na fetur a rana. Daga ciki, lita miliyan 28.50 aka kai kasuwar Najeriya, yayin da aka fitar da lita miliyan 15.47 zuwa kasashen waje.
A bangaren dizal, matatar ta samar da lita miliyan 24.32 a rana, amma ta fitar da miliyan 15.91 kasashen waje tare da kai miliyan 8.14 kasuwar cikin gida.
Bayanan sun kuma nuna cewa matatar ta yi aiki sama da karfin ganga 650,000 da aka tanada mata a asali. Kamfanin ya ce an kara karfin matatar zuwa ganga 700,000 a rana.
Wannan ci gaban ya nuna karuwar rawar da matatar ke takawa a kasuwar man fetur ta duniya, amma kuma ya tayar da tambayoyi kan yadda karuwar sarrafa mai a Najeriya za ta taimaka wajen tabbatar da wadataccen mai da farashi mai sauki a cikin gida.




