Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar da sabon jerin ‘yan takarar shugaban kasa da mataimakansu domin babban zaben Najeriya na Janairun 2027.
Takardar da Sakatariyar INEC, Rose Oriaran-Anthony, ta sanya wa hannu ta jera jam’iyyun siyasa 19 da bayanan ‘yan takararsu.
A karkashin jam’iyyar APC, Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai nemi wa’adi na biyu tare da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar zai tsaya takara a karkashin ADC, yayin da tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, zai kasance abokin takararsa.
Tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, yana cikin jerin a matsayin dan takarar NDC, tare da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin mataimakinsa.
Dan takarar AAC shi ne Omoyele Sowore tare da Haruna Garba Magashi. Jam’iyyar PDP ta tsayar da Sandy Ojang Onor tare da Babangida Umaru, yayin da Donald Duke da Mohammed Sule za su tsaya a karkashin PRP.
Sauran sun hada da Adewole Adebayo na SDP tare da Usman Muhammed Bugaje, da kuma ‘yan takarar wasu kananan jam’iyyu.
A bangaren jam’iyyar “A”, takardar INEC ta nuna kalmar “Court Order” a wuraren sunayen dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa, ba tare da bayyana sunayensu ba.
Za a gudanar da zaben shugaban kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa ranar 16 ga Janairu, 2027, kamar yadda jadawalin INEC ya nuna.




